Boma Bomai Biyu Sun Kara Tashi A Garin Patiskum.

Mutane na kallon wajenda Bom ya fashe

A yau Lahadi da missalin karfe uku da minti goma na rana, bom ya tashi a kasuwar ‘yan Jagwal inda ake saye da sayarwar wayayoyin hannu dake garin Patiskum.

Bisa bayanan da muka samu a halin yanzu dai nanunin cewar, wasu ‘yan mata ne guda biyu dauke da bama bamai sukayi kokarin shiga cikin kasuwar wayoyin hannu ta Jagwal, sai aka hana su shiga bisa cewar ana tantance mutane masu shiga kasuwar, dalilin haka suka koma suka shiga cikin keken nan mai tayoyi uku NAPEP ko kuma ince adaidaita sahu, suna cikin tafiya akan keken ne bom ya tashi harma wata mota dake kusa da gurin itama ta kama da wuta.

Har yanzu dai hukumomin tsaro basu fito sunyi bayani ba akan wannan tashin boma boman ba. A halin yanzu dai baza’a iya tantance mutane nawa ne suka rasa rayukansu dalilin wannan hari, mun dai sami labarin matan da suka kai harin da mai tukin a dai dai ta sahu, har ma da mai motar dake kusa alokacin tashin bom din duk sun mutu.

Wannan harin na biyu kenan a kwana biyu a garin na Patiskum, kasancewar a jiya muka baku rahotan tashin wani bom daya kawo ajalin wasu ‘yan sanda biyu.

Hakalin mutanen Patiskum dai a tashe yake domin a jiya nan suka gane wani mahari inda suka kira jami’an tsaro kuma aka kame shi domin bincike, alokacin binciken motar mutumin ne bom ya tashi inda ‘yan sanda biyu suka rasa rayukansu da jikkata mutane da dama.