Brazil Na Kara Kyau Gabannin Wasan Farko Na Cin Kofin Duniya
Brazil
WASHINGTON, DC —
Kocin Brazil Luiz Felipe Scolari na farin ciki da yadda kungiyar kwallon kafar Brazil ke kara kyau gabannin wasan farko da zata doka a gasar kofin duniya dake karatowa a mako mai zuwa.
Bayan cinye Panama da ciya-ciyyay 4 da babu a wasan sada zumunci na biyun karshe kafin gasar, Scolari yace dole sai an kara yin wasu ‘yan gyare-gyare, amma a tunaninshi kamar kungiyar tana kan hanyarta na shiryawa wasan farko da kasar Croatia a kwanaki 8 masu zuwa.
Scolar yace har yanzu yana dan damuwa, amma ba kamar kwanakin baya ba. Yace yana da karfin gwiwar cewa idan kungiyar ta cigaba da kara kyau, to zata yi wasa mai kyau a wasan na farko a gasar kofin duniya.
Wasan karshe na tsuma jini da Brazil zata yi da Serbia ne, ranar Juma’ar nan mai zuwa.
Zakarun kungiyoyin Spain, Atletico Madrid tace gola Miguel Moya ya amince ya bar kungiyarshi ta Getafe, domin zama dan Atletico.
Zuwan Moya yanzu zai baiwa golan Belgium Thibaut Courtois damar barin Atleticon bayan tsare mata raga na tsawon season uku, bayan da aka aro shi daga Chelsea.