Chelsea Ta Karrama Didier Drogba - Ta Doke Kungiyarsa ta Galatasaray - 20/3/2014
Magoya bayan Chelsea a bayan wani makeken kyalle na tunawa da tsohon dan wasansu Didier Drogba, lokacin da yaje a matsayin dan wasan Galatasaray domin gasar cin kofin Zakarun Kulob na Turai Talata 18 Maris, 2014
Wata mai gotyon bayan kungiyar Chelsea rataye da kyalle mai hoton rtsohon dan wasan Chelsea wanda ya koma Galatasaray, Didier Drogba, lokacin da kungiyoyin biyu suka kara a Stamford Bridge, Talata 18 Maris 2014
Didier Drogba na Galatasaray ya rungumi tsohon abokin wasansa a Chelsea, John Terry, a karshen karawar da suka yi a gasar cin kofin Zakarun Kulob na Turai a filin wasa na Stamford Bridge dake London, Talata 18 Maris, 2014
Didier Drogba na Galatasaray da Samuel Eto'o na Chelsea su na gaisawa da juna kafin karawar da kungiyoyin nasu biyu suka yi a Stamford Bridge Talata 18 Maris, 2014
Alkalin wasa Felix Brych, yana nunawa Didier Drogba na kungiyar Galatasaray, katin jan kunne a karawarsu da Chelsea, Talata 18 Maris 2014