Cin zarafin iyali rikicine dake faruwa tsakanin ma’aurata a gidajensu wanda ya hada da duka kokuma raunata daya daga cikinsu, fya’de, tsoratarwa da sauransu.
A wani rahotton Majalisar Dinkin Duniya yace, a duk mata uku daya na fama da matsalar cin zarafi, shidai cin zarafinnan amfi samun shine tsakanin ma’aurata ko wadanda suka shaku, inda kimanin mata miliyan dari shida da uku ke fama dashi.
A Najeriya kuma yara da mata wanda shekarunsu yake tsakanin sha hudu zuwa ishirin da hudu ke fama da matsalar cin zarafi, wanda ya hadar da duka, tsamgwama, zagi da fa’de a tsakanin ma’aurata.
Shugabar ma’aikatar kare hakkin dan adam kuma mai kula da shiyar arewa maso yamma Barista Hauwa Salihu Jauro, tace daga watan janairun wannan shekara kawo yanzu sunsami matsalolin mata guda hamsin. Kamar dai yadda masana ke fadi cin zarafi na tarwatsa gida kuma babu wanda ya cancanci cinzarafi domin kuwa baya ga tarwatsa gida da abin ya keyi, bai tsaya kan wanda abin ya shafa kadai ba yana da tasiri ga al’umma baki daya.
Your browser doesn’t support HTML5
Cin Zarafin Mata Na Tarwatsa Gida - 2'23"