Dalilin Da Ya Sa CNN Ta Sallami Don Lemon

Don Lemon (AP)

A ranar Litinin CNN ta sanar da sallamar Lemon, wanda shi ma ya sanar a shafinsa na Twitter cewa ya kadu da korar da CNN ta yi masa.

Kafar yada labarai ta talbijin CNN ta kori dadadden ma’aikacinta Don Lemon.

Korar Lemon na zuwa ne watanni biyu bayan da ya nemi afuwar masu kallon tashar kan wasu kalamai da ya yi game da ‘yar takarar mukamin shugaban kasar karkashin jam’iyyar Republican Nikki Haley.

A ranar Litinin CNN ta sanar da sallamar Lemon, wanda shi ma ya sanar a shafinsa na Twitter cewa ya kadu da korar da CNN ya masa.

Lemon ya ce ejansa ne ya fada masa sallamar da aka masa. Shekaru 17 ya yi yana aiki da CNN.

Gidan talbijin din na CNN bai yi bayani kan tafiyar Lemon ba, amma a tsakiyar watan Fabrairu aka yi ta caccakarsa bayan da ya ce shekarun Haley “sun ja.” 51.

Daga baya ya fito ya nuna nadama kan kalaman nasa.