Dalilin Da Ya Sa Muka Kama Mawaki Portable – ‘Yan sanda

Hukumar Kula Da Ayyukan ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kori Wasu Manyan ‘Yan Sanda Bakwai, Da Rage Mukami Wasu

Rundunar ‘yan sanda jihar ta Ogun ta ce ta ba Portable wa’adin sa’a 72 ya mika kansa amma ya ki.

‘Yan sanda a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya sun ce mawaki Portable na fuskantar tuhume-tuhume guda shida.

A ranar Juma’a hukumomin tsaro suka kama mawakin.

Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a ranar Talata, ya nuna yadda Portable yake sa-in-sa da wasu ‘yan sanda bayan da aka tura su shi kamo shi a wani dakin shan barasa da ya mallaka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun Muyiwa Adejobi ya ce ana zargin Habeeb Okikiola wanda aka fi sani da Portable da dukan wani mutum.

“Za a kai shi kotu, inda za a tuhume shi da laifin dukan wani mutum a Otta, wanda ya rubuta takardar korafi ga kwamishinan ‘yan sanda.

“Akwai tuhume-tuhume da dam akan ya doki wasu mutane, kuma za mu gudanar da bincike saboda korafin da jama’a suka yi.”

Rundunar ‘yan sanda jihar ta Ogun ta ce ta ba Portable wa’adin sa’a 72 ya mika kansa amma ya ki.

Hakan ne kuma ya sa aka kama shi baya da ya ki amsa gayyatar ‘yan sandan jihar ta Ogun.