Duka 'Yan Nijer Mazauna Amurka Ne Su Ka Yi Zanga-Zangar Lumana, Ko A'A?

Shugaban Nijer Mahamadou Issoufou

Wasu 'yan Nijer sun ce su duka ne suka yi zanga-zangar lumana a birnin New York, wasu kuma sun ce ba haka batun ya ke ba
Mataimakin shugaban kungiyar 'yan kasar jamahuriyar Nijer mazauna Amurka, malam Issa Gado wanda ke birnin New York ya ce a yau asabar sun yi zanga-zangar lumana a kofar ginin Majalisar Dinkin Duniya domin jan hankalin shugabannin Nijer kan matsalolin da ke addabar kasar yanzu haka:

Your browser doesn’t support HTML5

Issa Gado mataimakin shugaban kungiyar 'yan Nijer a New York.-1':32"


Amma da yake maida martani game da wannan batu na cewa duka 'yan kasar Nijer mazauna Amurka ne su ka yi zanga-zangar lumanar, malam Moutari alhaji Garba Azzarori Madaoua shugaban jam'iyar PNDS Tarayya a birnin Harrisburg, jahar Pennsylvania ya ce babu wani dan kasar Nijer mazaunin Harrisburg da ya je New York da sunan yiwa gwamnatin kasar zanga-zangar lumana:

Your browser doesn’t support HTML5

Moutari alhaji Garba Azzarori Madaoua shugaban PNDS a Harrisburg.-1':20"


Halima Djimrao ce ta tattauna da Malam Issa Gado da kuma malam Moutari alhaji Garba Azzarori Madaoua.