Dan Kunar bakin wake Ya Halaka Mutane 21 A Masar

'Yan kwana kwana da da jami'an tsaro a Masar,a wani Coci 'yan darikar Coptic inda wani dan unar bakin wake ya kai hari.

Wani jami’I a Masar yace bisa dukkan alamu wani dan kunar bakin wake da kafa ne ya kai hari kan wata majami’ar da ake kira Coptic da ya halaka mutane 21 d a safiyar yau Asabar.

Wani jami’I a Masar yace bisa dukkan alamu wani dan kunar bakin wake da kafa ne ya kai hari kan wata majami’ar da ake kira Coptic da ya halaka mutane 21 da safiyar yau Asabar.

Da farko hukumomin kasar sunce dan kunar bakin wake da mota ne ke da alhakin kai harinda ya jikkata mutane da dama a birnin Alexandria dake arewaci.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar tace akwai shaidar da take nuna cewa da hanun ‘yan ketare a kai wan nan hari.

Shugaban Masar Hosni Mubarak ya yi kira ga ‘yan kasar baki daya musulmi da kirista su mike tsaye kan abinda ya kira ta’addanci irin wanda aka kaiwa cocin Copti cikin dare.

Mr. Mubarak ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda wan nan hari ya rutsa dasu.

Harin ya auku ne minti talatin kamin kamin shigar sabuwar shekara,inda kiristocin suka hallara domin addu’oi na musamman. Babu wanda ya dauki alhakin kai harin,wanda bayansa ne kuma musulmi da kiristoci suka kara.