Matsalar Bakin Haure a Turai

Sojoji da 'yan sandan kasar Macediniya na kokarin ganin ana bin ka'ida yayinda bakin haure ke shiga jirgin kasa kusa da birnin Gevgeliji.
 

'Yan gudun hijira da bakin haure na jira don tsallaka iyaka, daga garin Idomini na kasar Girka zuwa kudancin Macediniya.

 

Wani dan sanda ya bugi wani mutum a lokacin da ya ke kokarin tabbatar da oda, a lokacin da bakin haure ki jiran jirgin kasan da zai kai su sansaninsu na wucin gadi.

 

Wani dan gudun hijra ya runtuma da gudu bayan da ya shiga yankin kasar Hunagary ta hanyar tsallake shingen da aka kafa na wucin gadi a wajen iyakar kasashen Hungary da Serbiya.
 

Wani dan gudun hijira na neman kayan sawa a tashar jirgin kasa ta Keleti dake Budepest a Kasar Hungary.
 

'Yan gudun hijira na kokarin tsallakawa ta karkashin shingen dake kan iyakar Serbiya da Hungary.
 

'Yan gudun hijira da bakin haure na zanga-zanga don a gaggauta yi masu rijista da kuma yi masu takardun shiga da fita. 
 

Masu aikin sa-kai na taimakawa 'yan gudun hijirar Syriya wadanda suka ji jiki
 

ሃገራዊ ምርጫ ኬንያ

Wani gungun 'yan gudun hijira daga Syriya na tafiya, inda suka doshi arewacin Demark.
 

북한이 대륙간탄도미사일(ICBM) 화성-14 시험발사 성공을 기념해 새 우표들을 발행했다. 화성-14 미사일이 발사대에서 준비되는 과정부터 발사 후 대기권 밖으로 벗어나기까지 단계별 모습을 보여주는 그림이 우표로 만들어졌다.

Ma'aikatan agaji na duba kayayyakin jinkai na 'yan gudun hijira a iyakar Hungary da Austria.

 

'Yan gudun hijira na cin abinci a sansaninsu, a Birnin Munich na kasar Jamus.
 

Gadajen da 'yan gudun hijira ke kwanciya a sansaninsu a Birnin Munich na kasar Jamus.