Fim Din "Tsakaninmu" Ya Yi Cinikin Sama Da Miliyan 3 A Mako Biyu

Hoton fim din "Tsakaninmu" (Hoto: Istagram/real-ali-nuhu)

"Wannan babbar nasara ce, duba da fim din ya fita ne ba a lokacin hutu ba, kuma a daidai lokacin da sinima take zazzabi na rashin masu kallo."

Fim din "Tsakaninmu" ya yi cinikin naira miliyan 3.2 cikin mako biyu da aka fara haska shi a sinima a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya a cewar Ofishin Box Office Kannywood.

An fara nuna fim din ne a ranar 26 ga watan Maris.

"Tsakaninmu ya hada kudi Naira Miliyan Uku da dubu Dari biyu da Casa'in da da takwas da Dari biyar (N3, 298, 500) cikin sati biyu." Ofishin box office na Kannywood da ke tattara bayanai kan yadda fim ya karbu a wurin masu kallo da yawan tikitin da aka sayar ya wallafa a shafinsa na Instagram a karshen makon da ya gabata.

A 'yan watannin nan, fina-finan masana'antar Kannywood da ake sake wa, sun fuskanci matsalar annobar korona, wacce take takaita tarukan jama'a, amma bayan da hukumomi suka sassauta matakan, al'amura sun dan daidaita.

"Wannan babbar nasara ce, duba da fim din ya fita ne ba a lokacin hutu ba, kuma a daidai lokacin da sinima take zazzabi na rashin masu kallo...... saboda cutar Coronavirus." Ofishin na box office Kannywood ya ce.

Ya kara da cewa, hakan na nufin fim din na "Tsakaninmu," wanda ya ta'allaka kan soyayya da takaddamar zamantakewa, ya shiga jerin fina-finan da suka hada kudi "masu nauyi" a cikin sati biyu.

"Hakan alama ce da ke nuna fim din ya samu karbuwa a wajen 'yan kallo, kuma shi yake nuna girma da isa ta masu shirya fina-finai."

Fim din na Tsakaninmu" wanda jarumi Ali Nuhu ya ba da umurni, Abubakar Bashir Mai Shadda ya shirya, ta tattaro manyan jarumai irinsu, shi kansa Ali Nuhu, Abba Al Mustapha, Baballe Hayatu, Yakubu Muhammed, Umar M. Shariff, Maryam Booth, Maryam Yahaya da sauransu.

Ga jerin sunayen fina-finan da suka hada kudi na miliyoyin nairori cikin mako biyu a cewar ofishin na Box Office Kannywood:

- Mati A Zazau - N4, 489, 400

- Hauwa Kulu - N3, 562, 000

- Kar Ki Manta Da Ni - N3, 474, 100

- Tsakaninmu N3,298, 500

- Bana Bakwai - N3, 180,000