Fiye da Mutane Milyan Biyu ke Mutuwa Sanadiyar Cutar Kiba
Cutar Kiba
WASHINGTON, DC —
Lallurar kiba fiye da kima lallura ce da jikin dan Adam, ke tattare da maiko, fiye da kima, wanda kuma yake shafar lafiyar, dan Adam.
Wannan lallura kan faru ne sanadiyar cin abinci masu gina jiki, fiye da yadda yakamata, kuma batare da matsa jiki ba koda yake kiba ga wasu gado ne, duk da haka kiba na cutar da lafiyar dan Adam, kuma likitoci na jan kunne akai.
Hukumar lafiya, ta duniya, tace lallurar kiba na daga cikin matalolin dake haifar da ciwon hawar jini, rashin sinadarin dake kare cututtuka, masamman ga masu ciwon sukari, dama wasu cututtuka na daban wadanda alkaluma sun nuna cewa fiye da mutane milyan biyu ne ke mutuwa a kowace shekara, sanadiyar cutar kiba a duniya.