Goodluck Jonathan Yayi Alkawarin Inganta Tattalin Arzikin Najeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Shugaba Goodluck Jonathan, yayi alkawarin inganta tattalin arzikin Najeriya, in har ‘yan Najeriya, sun sake zaben sa a karo na biyu.

Yayi wannan alkawarin ne a wajen gaggamin yakin neman zabe da aka gudanar a Jos babban birnin jihar Filato, ya kuma yi alkawarin inganta aikin noma, masamman noman rani, don matasa su samu aiyukan yi.

A nashi jawabin shugaban jam’iyyar PDP, na kasa Alhaji Adamu Mu’azu, ya bayyana nasarorin da shugaban kasar ya samu da suka hada da kawar da cutar Ebola, ya kuma bukaci jama’ar, jihar Filato, dasu zabe jam’iyyar PDP, batare da banbanci kabila ko addini ba.

Shi kuwa mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, albishir ya yiwa jama’ar, jihar Filato, kan cewa jirgin kasa zai fara sintiri a mako mai zuwa daga Jos, zuwa sassa daban-daban na Najeriya.

Gwamna jihar Filato, Jonah Jang, ya bukaci shugaba Jonathan, daya umarci hukumar zabe data amincewa wadanda basu sami katin zabe na dindindin ba yin amfani da katin zabe na wucin gadi a zabe mai zuwa kasancewar mutane da dama basu sami katin zaben na dindindin ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Jonathan a Jos - 2'50"