Gwamnan Farin Kaya Na Farko A Bayelsa Ya rasu

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha (R), Abuja, May 29, 2013.

Tsohon gwamnan farin kaya na farko a jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha ya rasu jiya a asibitin koyarwa na jami’ar Patakwal sakamakon bugun zuciya.

A wata sanar da gwamnatin jihar Bayelsa ta bayar da sa hannun Mr Daniel Maxson, an bayyana marigayin a matsayin jigo a siyasar jihar. Sanarwar tace rasuwar tsohon gwamnan babban rashi ne ga gwamnati da kuma al’ummar jihar Bayelsa.

Dangin marigayi Diepreye Alamieyeseigha sun bayyana shi a matsayin gwarzo mai kishin al’ummarshi da ci gaban jihar.

Wani mazaunin Amasoma mahaifar tsohon gwamnan da wakilinmu Lamido Abubakar yayi hira da shi, ya bayyana cewa, tunda aka sanarda rasuwarsa kusan sai kace al’amura suka tsaya, yayinda jama’a suka shiga wani yanayin makoki kasancewarsa ba a yankin da ya fito kadai ba, amma a jihar baki daya an daukeshi a matsayin jigo a harkokin siyasar jihar.

A baya bayan nan hukumomin Birtaniya suka nuna niyar neman gwamnatin Najeriya ta tasa keyarshi zuwa kasar domin amsa zargin hallalta kudin haram da aka tuhumeshi da aikatawa, kafin ya yi shigar mata ya sulale ya koma Najeriya, zargin da ya musanta.

Ga cikakken rahoton

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton Rasuwar Alamieyeseigha-3:37"