Gwamnati Zata Taimakawa Mutanen Mubi

Mata na Adua'a bayan Harin bom

Gwamnatin jihar Adamawa,tayi tir da harin da aka kai garin Mubi,ta kuma yi alkawarin taimakawa wadanda suka jirkata da kuma wadanda suka rasa dukiyoyinsu.

Darakata yada labarai na gwamna jihar ne ya furta haka, ya kuma yi kira ga jama;a jihar cewa duk inda aka mota ko jaka wanda ba’a san abunda yake ciki ba a sanar da jami’an tsaro.
Ya kara da cewa duk mutumin da ba'a ganewa ba ko kuma harkokinsa nada ayar tambaya to a tabbatar da cewa an sanar da jami'an tsaro.

Koda yake al’amura suka fara kwantawa a Mubi bayan tashin bom,rahotani na nuna cewa kawo yanzu addadin wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka samu munanan raunuka na karuwa.

Kamar yanda mazauna garin na Mubi ke cewa addadin wadanda suka rasa rayukansu yafi wanda hukumomi suka bada.

Hare-haren ‘yan bindiga na karuwa cikin kwanakin nan a jihar Adamawa, masammam a yankunan Madagali ,dake makwabtaka da jihar Borno.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnati Zata Taimakawa Mutanen Mubi - 2' 46"