Gwamnatin jihar Kano ta sallami ma’aikatan wucin gadi

Gwamnatin jihar Kano ta sallami ma’aikatan wucin gadi dubu biyu da dari shida da ishirin bayan sun kwashe shekaru takwas suna aiki a hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar, sai dai kungiyar kwadago ta najeriya reshen jihar Kano ta kalubalanci matakin.

A cikin hirarshi da manema labarai. Kwamishinan watsa labarai na jihar Kano Mohammed Garba ya bayyana cewa, akwai amaja da kuma rashin gaskiya a aikin ma’aikatan, bisa ga cewarsa, basu gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, Yace gwamnati ta lura akwai rashin gaskiya wajen biyan ma’aikatan sabili da haka aka yanke shawarar soke tsarin bayan gudanar da cikakken bincike kuma a sake daukar wadansu sababbin ma’aikata da zasu gudanar da aikin yadda ya kamata, ma’aikata wadanda suke da akida da kuma zasu gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ma’aikatan sun koda da wannan matakin da gwamnatin ta dauka na dakatar da ma’aikatan da cewa, bata yi masu adalci ba, tare kuma da kira ga gwamnatin ta sake nazarin batun da maida su bisa aiki.

A nata bangaren, kungiyar kwadago ta jihar Kano tace zata jajirce taga cewa, an yiwa ma’aikatan adalci.

Shugaban kungiyar kwadagon reshen jihar Kano yace kungiyar kodago ta duniya ILO ta haramta daukar ma’aikatan wucin gadi na tsawon lokaci ko a kamfanoni masu zaman kansu balle gwamnati saboda haka ba zasu yi kasa a guiwa ba wajen ganin bayan wannan tsarin a jihar Kano.

Ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano, Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kano POVs-2:44"