Gwamnatin Ukraine Zata Murkushe Borin 'Yan Tawaye

'Yan tawaye dake goyon bayan yankinsu ya hade da kasar Rasha

Gwamnatin kasar Ukraine ta ce Jumma'annan zata kawo karshen mamaye gine-ginen gwamnatin da 'yan aware masu goyon bayan Rasha suka yi a kusa da kan iyakar Rasha, ko ta hanyar tattaunawa ko ta hanyar yin amfani da karfi.

Da ya ke magana game da kiki-kakar da ake yi a biranen gabashin kasar na Luhansk da Donetsk, ministan harakokin cikin gidan kasar Ukraine, Arsen Avakov, ya fada a jiya Laraba cewa :" masu son a tattauna, mu na yi mu su tayin tattaunawa da kuma warwarewa ta hanyar siyasa, 'yan tsirarun da ke son fada kuma, za su samu amsa mai tsananin karfi."

A jiya Laraba gwamnatin kasar Ukraine ta yi wannan kashedi, a lokacin da jami'ar diflomasiyar Amurka, Victoria Nuland ta shaidawa wani kwamitin majalisar dokokin Amurka cewa a tsanaki aka shirya mamaye gine-ginen, cikin kyakkyawan tsari, da kuma sanin wuraren da ya kamata a zaba. Haka kuma ta ambaci kwakkwarar shaidar cewa da hannun Rasha a ciki, sannan ta yi gargadi game da abun da zai biyo baya idan aka bari aka yi rikicin ba a shawo kan sa ba.