An zargi Gwamnonin PDP, da suka canja sheka zuwa APC, da yin butulci ga jam’iyyar PDP, masamman ma Gwamna Sokoto Aliyu Wamako.
Gwamna jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ne ya furta haka a lokacin da yake jawabi a wurin gaggamin yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan, a Sokoto.
Yace “ An zabi Wamako, an kai karar sa aka soke zabe muka zo wannan wuri, da ake cewa PDP, jam’iyyar, azzalumai, ce ta masu kama karya, wannan jam’iyyar, tayi amfani da kama karya, ya zauna a wannan mulkin nasa, a lokacin su ayin kama karya an sasu, idan kama karya aibi ne, ai an kama an karya an basu.”
A nasu martanin jam’iyyar APC, ta bakin daya daga cikin manyan dattawan jam’iyyar, APC, a jihar Sokoto, Dr. Abubakar Muhammadu Sokoto, yace “ Ina ganin wadannan maganganun da Sule Lamido, yayi shi yakamata ya zama mutu na karshe da zai yi irin wannan maganar, dalili tafiyar nan dashi aka fara amma ana tsakiyar yinta sai rikici ya taso na maganar dansa da aka kama da rashin gaskiya, dole sai ya koma cikin wadan can wadanda ke kare marasa gaskiya domin kare marasa gaskiya shine akin su, saboda haka cewa wani yayi butulci ba daga gareshi ba.”
Your browser doesn’t support HTML5
Goodluck Jonathan a Sokoto - 2'56"