Hukumomin Najeriya, sun musanta rade-radin da ake yi na ko an bada ko an hanawa sojojin kasashe makwabtan Najeriya, shugowa kasar domin su taimaka wajen yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram.
Mr. Mike Omeri, shugaban cibiyar, bayar da bayyanai akan yaki da ta’addanci, a Najeriya, ne ya bayyana haka a wata hira da suka yi da wakilin mu Umar Faruk Musa a Abuja.
Yace ana ta bada bayyanai masu sabani wadanda bana gaskiya bane, abunda ke zahiri, Gwamnatin Najeriya, na daukar duk matakin da yakamata kuma tana hada gwiwa da kasashe makwabtan ta domin a tabbatar da cewa an samu galaba akan wannan yaki da ake yi da ta’addanci a cikin Najeriya.
Babu shakka yanzu ‘yan Najeriya, sun sa rai fiye da ko wani lokaci cewa an kusa kawo karshen wannan matsalar ta’addanci. Bayan dai Najeriya, da kasashen makwabta, suna tarurruka da hadin gwiwar tabbatar da ganin cewa an yaki ta’addanci, majalisar Dinkin Duniya, ta fito filin ta nuna cewa zata dauki duk matakin da yakamata domin a kawo karshen wannan matsalar da gaggawa.
Your browser doesn’t support HTML5
Boko Haram - 4'05"