Italy ta Kira Rossi da Cassano - 12/4/14

Dan wasan AC Milan, Antonio Cassano.

An kira Giuseppe Rossi da Antonio Cassano akan zuje a auna lafiyarsu da kuzarinsu domin tantancewa ko zasu iya buga wasannin zakarun kasashen duniya, wato World Cup a turance, kuma mai koyar da kungiyar Italy, Casare Prandelli shine yayi wannan kira. Sai dai Matta Destro wanda yake wasa sosai yanzu, ba’a kira shi ba, saboda dakatar da shi da akayi a wasannan Serie A har guda uku.

Coach Prandelli yanzu ya saka za’a auna lafiya da kwarewar ‘yan wasa 42 ranar litinin da Talata a filin horon kwallon kafa na kasar dake birnin Fluorence a can Italy. Horon da za’a yi musu, zai hada da saka ‘yan wasan a cikin yanayi mai zafi kamar kasar Brazil, domin jikinsu ya fara sabawa da irin wannan yanayi.