Jamiyyar adawa ta APC, a shiyar arewa maso gabas tace ba gudu ba jadabaya, dangane da batun gudanar da zabe, na kasa da za’a yi a wannan shekarar.
Wannan matsayi da jamiyyar ta dauka na kunshe ne a jawabin bayan taro ne, wanda Gwamna Borno, Kashim Shettima, ya kasance shugaban taron yace” batun zabe babu wani taimakon da ake mana hakkin mune mu zaba kuma a zabe mu wannan yana cikin kundin tsarin mulki.”
Ya kara da cewa “ Ba’a kanmu aka far aba akwai mutanen Okirka, da aka kais u Port Harcourt suka yi zabe, akwai mutanen Wusa a Taraba da aka kawo su sun yi zabe ba’a garin su ba, za’a yi zabe insha Allah.”
Dan kwamitin amintattu na jamiyyar ta APC, kuma dan takarar sanata, daga jihar Gombe, Bayero Nafada, yace in dai mutun dan kasa ne akwai tanadi a kundin tsarin mulkin kasa dole a bar su suyi zabe.
Your browser doesn’t support HTML5
Zabe a Arewa maso gabas - 3'25"