Jam'yyar APC Tace a Kasa a Tsare Kuma Raka

Muhammadu Buhari

Sashen matasa na magoyan bayan janar Muhammadu Buhari, sun gudanar da wani gangami a Abuja, don jan hankalin sauran matasa, da’a maida zuciya nesa a yayin tunzurin kamfe.

Taron wani mataki na kuacewa fitina masamman a yanzu da askin zaben 2015, yazo gaban koshi.

Ibrahim Dasuki Jallo Waziri, shugaban matasan APC, na kasa yace “Babu abunda zaka same shi in ba cikin kwanciyar hankali ba, domin duk abunda zakayi ya zamana anyi aikin ashsha ba zai kawu mana ci gaba ba, ba zai kuma kawo mana alheri ba, jama'a, su tabbata anyi wannan zabe lafiya.”

Ya kara da cewa bayan sun jefa kuri’a, zasu tsare, su raka kuma su jira har sai an fadi sakamako zabe domin kujewa magudi.

Dattijo kaftin Bala Jibirin, yayi harsashen APC, zata lashe zaben, yana mai cewa ‘yan PDP, su san mulki Allah ke badawa, su kuma san cewa lokacin kashen mulkin su yazo.

A gefe daya kuma jigogin PDP, na ganin mukarraben Buhari, ‘yan abi Yerima ne asha kida.

Adamu Maina Waziri, dan takarar Gwamna na jihar Yobe, yace a wannan yunkuri dole a banbanta wadanda suke hamayya damu, da kuma jagoran ‘yan jam’iyya, hamayya ta kasa baki daya.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan APC - 2'57"