Janar Buhari Yace Kudade da Zamu Samu ba Kananan Kudade Bane

Muhammadu Buhari

A jihar Zamfara dubun dubatan jama’a, ne suka yi zamar durshan suna jiran isowar dan takarar shugaban kasa, na jam’iyyar adawa ta APC janar Muhammadu Buhari, inda jiran nasu yazo karshe misali karfe goma na dare, a lokacin da dan takarar ya isa garin Gusau.

A jihar Kebbi, kuma baya da dubban jama’a, da suka hallara, a dandalin wasani na Haliru Abdu, dake birnin Kebbi, wasu daruruwane suka yi tattaki da kafa na tsawon kilomita fiye talatin da biyar, daga garin Jega zuwa birnin Kebbi, domin jaddada kaunarsu ga janar Buhari.

Daya daga cikin wadanda suka yi wannan tattaki daga Jega zuwa birnin Kebbi, Sanusi Daudu Jega, yace “ Ba mota ne bamu da ba ko kuma kudi shiga mot aba mun yi wannan ne don mu nunawa Najeriya, da Duniya cewa muna iya yin dukkan abunda ya wajaba gad an siyasa gad an takara domin mun tako daga Jega zuwa birnin Kebbi kilomita talatin da shida, shine muke so mu nunawa Duniya muna iya zaman awowi talatin da shida domin hakkin kuri’un mu.”

A jawabinsa a jihohin biyu janar Buhari, ya bada karfi ne akan rashin tsaro, da rashin aikin yi da cin hanci da rashawa, yace " Matasa kokarin da za muyi shine mu koma mu gyara noma, kuma masu kananan sanao'i, a hada su da kanfanonin bada bashi, kudaden da zamu samu na hana cin hanci da rashawa ba kananan kudade bane, zamu yi amfani dasu mu sake gyara makarantu da kautatawa jami'an tsaro."

Your browser doesn’t support HTML5

Buhari Zamfara da Kebbi - 2'59"