Tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon mairitaya ya bayana cewa zai shiga tsakani domin a sami tattaunawa da ‘yan kungiyar Boko Haram, da gwamnatin kasar domin a samarda zaman lafiya a shiyyar arewa maso gabas wanda rikici ya addaba.
Janar Gowon yayi wannan ikirarin ne a wurin taron da hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya, wato [UNDP] ta shirya tare da hadin gwiwar wasu hukumomin gwamnatin taraiya da aka gudanar a garin Gombe.
Da yake jawabi a wurin taron Farfesa Al-Amin Muhammad, yayi bayani akan abubuwan dake haifar da kungiyoyin dake tada kayar baya.
Yace “ duk inda ya zamanto shugabanci ba’a yin adalci, dukiyar kasa bata zagayawa, duk inda ya zamo Malaman addini an barsu kara zube, duk ra’ayi da akidar da suke so zasu gabatar da ita duk inda ya zamanto ana yin zalunci da rashin gaskiya dole ne mutane su sami rashin jin dadi, daga nan idan aka sami wani wanda ya iya shiga gaba sai ya bada jagoranci sai a fara irin wannan tsageranci.”
Mai martaba sarkin Bauchi, Rilwanu Sulaiman Adamu, wanda ya wakilci Sarkin Musulmi, ya umarci jama’a da a fahimci juna a kuma rungumi zaman lafiya, batare da banbanci addini ko na kabilanci ba.
Your browser doesn’t support HTML5
shiga tsakani - 3'43"