Juyayin Kisan Kiyashin Yahudawa

Rahotanni na cewa harkokin yau da kullum sun tsaya Cik a Isra’ila yau litinin da safe, a dalilin bikin tuna zagayowar kisan gillar da aka yiwa Yahudawa miliyan shida a lokacin yakin duniya na biyu.
Dukkan motocin asibiti da na kai gawa binnewa sun bin kan tituna suna kada karrarwar juyayi,an kuma tura motoci na musamman suna zazzagaya kan titunan kowane sako tare da yin jawabin abinda ya janyo kisan gillar.

Motoci da sauran ababan hawa duk an tilasta masu tsayawa wuri guda ba gaba ba baya a lokaci guda. Su kansu masu tafiya a kasa sai sun tsaya na tsahon mintunan biyu a duk inda suke.

Wannan rana ta tunawa da kisan gillar Yahaudawa, itace ranar da Isra’ila ta kebe ta musamman domin yin juyayi da yin addu’oi a kowace shekara.

Za’a kuma karanta sunayen wadanda suka rasa rayukansu a wancan lokacin kisan gillar a majalisar dokokin Isra’ila.