Kaftin din Liverpool Steven Gerrard, na shirin barin kungiyar ta Liverpool, a karshen kakar kwallon bana, wanda yake a lokacin ne kwantraginsa da klub din zai zo karshe.
Dan shekaru 34, kuma dan wasan tsakiya ya kwashe shekaru yana bugawa Liverpool ta maula, amma a yanzu lokaci yayi na barin kungiyar.
Babu inkari dagane da hukumcin da Gerrard, ya yanke na barin kungiyar ta Liverpool, tsohon da kungiyar tasu wato Jamie Carragher, yace abun babu dadi amma yin hakan yayi daidai.
Koda yake Gerrard, yayi ritaya daga bugawa kasar Ingila kwallo, bayan gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, bai bara wasan kwallo ba.
Yana da tabbaci buga kwallo a wani klub, a zamaninsa, a Liverpool, ya jefa kwallaye 180, a raga, a wasani 695.
Your browser doesn’t support HTML5
Liverpool - 1'00"