Kamfanin shafin sada zumunta na Twitter ya fitar da rahotansa na karshen shekara, wanda ke nunin asarar da ya tafka kusan ninkin asarar da ya yi a karshen shekarar 2015.
Rahotan da kamfanin Twitter ya fitar na nuni da cewa baki ‘daya yayi asarar dala miliyan 167 a karshen shekarar 2016. A shekara ta 2015, kamfanin ya yayi asarar dala miliyan 90 a wancan shekarar.
Wani abin mamaki dai shine yawan mutanen da suka bude shafin Twitter ya karu da kaso 4 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2015, wanda yawan masu amfani da shafin ya kai mutane miliyan 319.
Twitter dai ta gaza tsayawa kafada da kafada da sauran kafafen sada zumunta irin su Facebook, wanda a kwanan nan kamfanin Twitter ma ya rage yawan ma’aikatansa kuma har da yunkurin fansar da kamfanin wanda bai sami nasara ba.
Shafin Twitter mai shekaru goma da kafuwa bai taba samun riba ba, sai dai anyi ta canza tsarin shafin, da kuma samun karuwa masu amfani da shi.
Your browser doesn’t support HTML5
Kamfanin Sada Zumunta Na Twitter Ya Tafka Asara - 1'09"