Yanzu haka,al’ummomin da hare-haren yan Boko Haram ya raba da gidajen su da sauran masu ruwa da tsaki, sun fara maida martani ga kalaman da gwamnan jihar Adamawa, Mr Bala James Ngillari yayi a wani taro na masu ruwa da tsaki da hukumar zabe ta yi da hukumomin jihohin Adamawa, Borno da Yobe, inda gwamnan Adamawan yayi kira da a dage zaben dake tafe a watan gobe, har zuwa watan Afrilu.
Alhaji Umaru Duhu , dan takara ne a inuwar jam’iyyar APC, a yankin Madagali, yace sun yi mamakin wannan kiran da gwamnan yayi na a dage zabe, ya kara da cewa bada yawunsu yayi ba.
Shi dai gwamnan Adamawan, wanda yanzu haka mahaifarsa ta Madagali ke hannun mayakan Boko Haram, na cikin yan takara a zaben dake tafe, inda jam’iyarsa ta PDP, ta bashi tikitin tsayawa takarar kujerar majalisar dattawa.
Your browser doesn’t support HTML5
Dage zabe - 3'08"