Koda Naira Biyar aka Maida Farashin mai mun san Inda Muka Dosa

Layin Mai a gidan man NNPC Mega Station

Biyo bayan rage farashin man fetur a Najeriya, wasu gidajen mai sun rufe sa’ilinan wadanda ke bude suna fama da dogaye layuka a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda wakilin muryar Amurka, Nasiru Adamu El-Hikaya, ya aiko mana.

Wanda haka ya baiwa matasa ‘yan bakar kasuwa damar cin karansu babu babbaka, inda suke sayarda man da tsada ga jama’a.

Koda dai mutane a Sokoto sun yi murna, babu wani abun na zahiri da ya canja, in ji Murtala Faruk San’ina, ya kara cewa, jama’a, sun ce abun da zai yi tasiri shine a maida farashin Naira sittin da biyar.

Bauchi, kuma in ji wakilin mu Abdulwahab Muhammad, sun yiwa lamarin fasarar siyasa ne inda wani yace koda Naira biyar aka maida farashin man su sun san inda suka dosa.

A Ibadan kuwa a jihar Oyo, bata canja zani ba inda wasu suka dangata rage farashin da siyasa, wasu kuwa suka ce rage farashin bai dame suba, domin a cewar su anyi haka ne domin a na neman kuri’ar su.

Jihohi masu fuskantar kalubalen tsaro zai yi wuya suji tasirin rage farashin a dan kankanin lokaci, in ji Haruna Dauda, a Maiduguri, inda yake cewa har yanzu gidajen mai basu bi umarnin Gwamnatin tarayya ba sai dai ma haifar da karancin man fetur din a gari.

Your browser doesn’t support HTML5

Tasirin Farashin Fetur - 3'03"