Koko da Kosai Na'iya Zama Sanadiyyar Shiga Aljannah

Kosan 'yan Gayu

Allah gatan bawansa, yakanyi hallitar sa yadda yaso batare da shawar ko tuntubaba, Malama Hadiza me kosan ‘yan gayu tayi karin haske na yadda ta samu kanta a rayuwar yau da kullun. Ta kasance tana da ‘yaya biyu da Allah ya jarabcesu da cutar Amosalin jinni wato “Sickle cell anemia” a turance, wanna wata cutace da take da wuyar sha’ani, a irin wannan haline yasa Malama Hadiza, take wannan sana’a na toya kosai, fanke da Koko, don ta samu yadda zata taimakama mijinta wajen daukar dawainiyar wadannan yaran guda biyu nasu masu dauke da wannan jarabawar.

Tayi nuni dacewar wannan wata cutace me bukatar kudi da yawa, wanda shikuma mijin nata ma’aikacin gwamnatine, idan watayayi nisa sukanshiga halin kakanikanyi, haka yasa take wannan sana’ar kuma Allah yasama sana’ar albarka matuka. A yanzu haka tasamu dammar bude asusun ajiya a banki don tara ribar wannan sana’ar, tunda batada yadda zatayi tasamu wani gudunmawa daga gwamnati ko wasu kafofi masu zamankansu, a sanadiyyar bata san kowaba.

Tayi kira ga ‘yan uwanta mata dasu tashi su kama sana’ar ko badan komai ba ko dan su taimakama ‘yayansu a rayuwa, domin tsakanin uwa da uba ba’a san gawar fariba, don haka kowa na iyazama cikin halin daukar nauyin yara, wanda idan mace bata iya sana’a ba to abun zai kai ga sata cikin wani hali na rayuwar yau da kullun.