Kungiyar Al Shabab ta kai hare hare guda biyu

Wani sojan Somaliya yana gadin wani wuri da yan Al Shabab suka kaiwa hari

An kashe akalla mutane 18 a hare haren bama bamai guda biyu dabam dabam da yan kungiyar Al Shabab suka kai a kasar Somaliya

Jami'an kasar Somaliya sunce akalla mutane goma sha takwas ne aka kashe jiya Asabar a kasar a hare haren bama bamai dabam dabam guda biyu, wadanda ake zato yan tawayen kungiyar Al Shabab ne suka kai.


A harin farko sojoji goma sha hudu ne aka kashe fiye da ashirin kuma suka ji rauni a lokacinda yan yakin sa kai suka tuka motar dake dankare d nakiyyoyi zuwa wani sansanin horas da sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika daga Kenya da kuma sojojin Somaliya a birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa dake kudancin kasar.


Sansanin soja yana cikin harabar jami'ar Kismayo inda ake horas da sojoji akan dabarun yakar yan tawaye. Kungiyar Al Shabab tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin a gidan rediyonta ta Andulus kuma tayi ikirarin cewa sojoji dari ne ta kashe.


To amma wani baban jami'in yan sanda a Kismayo Kanal Mohammed Hasan ya dage akan cewa sojoji goma sha hudu aka kashe aka jiwa guda tara rauni. Yace wasu da aka kwantar a asibiti sunji mumunar rauni.


Rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika ta sa wata sanarwar a shafinta na twitter inda tayi bayanin cewa an kashe yan yakin sa kai guda biyu a harin, aka kama guda biyu kuma yanzu haka jami'an tsaro suna yi musu tambayoyi.


Wani jami'in yan sanda mai suna Abdullah Osoblr yace hari na biyu an kai ne a Mogadishu baban birnin kasar inda aka kashe mutane hudu da raunana mutum goma. Yace bam din da aka boye cikin wata mota ya tashi ne kusa da wani ofishin yan sanda da kuma wani wuri da wadanda suka rasa matsuguninsu suke zaune.


Nan da nan babu kungiyar tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin a birnin Mogadishu kodayake yana da alamun kungiyar Al Shabab. Duk da cewa an samu nasarar tilasta musu ficewa daga manyan sansanonin ko kuma tungayensu, har yanzu kungiyar tana samu nasarar kaddamar da munanan hare hare akan baban birnin kasar da wasu wurare a kasar.