Kungiyar Izalatul bidi'a wa Iqamatis sunnah, ta jihar Bono, ta raba kayayyakin abinci, ga ‘yan gudun hijira fiye da dubu goma sha shida, da rikicin Boko Haram, ya raba da gidajensu, wadanda ke saune a gidajen mutane daba-daban a fadi jihar Borno.
Kungiyar tace ta dauki wannan matakin ne don rage wahalhalun da jama’a, ke fuskanta, masamman ma wadanda ke rike da ‘yan gudun hijira, a gidajensu.
Imam Baba Kura Gwani, wanda yake shine Mataimakin shugaban majalisar Malamai yace kungiyar, ta kashe kimamin Naira miliyan 60 wajen sayen kayyakin abinci, don tallafawa ‘yan gudun hijiran.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun yabawa kungiyar, da cewa taimakon zai tamaka wajen sauka masu kuncin rayuwa.
Your browser doesn’t support HTML5
Kungiyar Izala - 3'23"