Kungiyoyin Ma'aikatan Albarkatun Man Fetur Sun Fara Yajin Aiki

Layin Mai a gidan man NNPC Mega Station na Makurdi, Jihar Binuwai, Najeriya

Kungiyoyi manyan ma'aikatan matatar fetur da iskar gas a Najeriya wato PENNGASON da Kungiyar ma'aikatan mai da iskar gas ta kasa wato NUPENG sun shiga yajin aiki na sai baba yagani. Wannan yajin aikin zai sa rayuwar mutane da dama cikin wani hali, wanda da ga fara wannan yajin aikin har litar mai ta kai naira 250, a birnin tarayya Abuja.

Samari 'yan bakar kasuwa kuwa wannan wata damace wadda zasu samu kudi sosai. Shi kuma shugaban NUPENG Achiso Igwe, ya ce wannan matsalar tafi karfin shekara goma, kuma babbar matsala a nan itace, rashin kyara matatun mai, kamfanonin mai na kasashen waje a Najeriya na cin zarafin ma'aikata wanda basu son daukan ma'aikata na dindindin, sai na wucin gadi, kuma idan har ma'aika sun shirya yin zanga zanga na nuna kinyarda da wani take haki, sai a sa jami'an tsaro su tarwatsasu. Wannan da wasu matsaloli sune suka sa suka ga yakamata su shiga yajin aiki don gwamnati ta duba wadannan bukatun.

Mutane dai sunyi korafi dangane da matsalar da talaka zai fuskanta a kasar a sanadiyyar wannan yajin aikin. Ganin cewar miliyoyin 'yan najeriya na fuskantar matsatsi na rayuwa wanda akasarin wasu basu samun kudi da yakai kimanin dallar Amurika $1 wanda yayi dai dai da naira 180 a rana daya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Ma'aikatan Mai