Kwana Da Jarirai Yakan Taimaka a Shayar Da Su Da Nonon Uwa

Shayar Da Nonon Uwa.

Wani rahoton da aka yi a yi a jihar New York ya nuna cewa kwana da jarirai a gado daya da iyayensu mata, yakan taimakawa iyayensu mata shayar da su da nono har zuwa lokacin da masanan lafiya suka tsara musu
Wani rahoton da aka yi a yi a jihar New York ya nuna cewa kwana da jarirai a gado daya da iyayensu mata, yakan taimakawa iyayensu mata shayar da su da nono har zuwa lokacin da masanan lafiya suka tsara musu.

Amma bisa ga binciken, kwanciya kan gado daya da jariri zai iya kawo hadarin mutuwar yara farat daya da ake kira da turance a takaice- SIDS.

Kwararrun likitocin masu kula da lafiyar jarirai na Amurka sun bada shawara cewa iyaye su sa ‘ya’ya kusa da su – kamar kwana a daki daya – koda yake ba gado daya ba, domin ya rage hadarin SIDS. Kimanin jarirai 2,500 suke mutuwa daga SIDS kowacce shekara a Amurka.

Majalisar dinkin duniya ta bada shawarar shayarwa har sai yaro yayi wata shida yana shan nono kadai, da kuma suna ci gaba da bada nono da abinci kala biyu har shekara biyu na yaro.

A lokacin binciken mata masu jarirai a shekarunsu na farko, an gano cewa shayarwar ta nono wata bakwai ne kawai. Shayarwar ta kai sati 10 kawai.

Binciken ya nuna cewa, kwanciya gado daya da mata ke yi da ‘ya’yansu yana taimakonsu su ba ‘ya’yansu nono sosai. An gano cewa mata dake kwana da yaransu sosai, fiye da wadanda basu kwana da jariransu.