Labaran Najeriya da Dumi-Duminsu - 11/03/2014

Motar sojan Najeriya a kofar wani gidan da aka kona a garin Bama

Karshenta dai, sojojin Najeriya sun fara kutsawa cikin dajin Sambisa, inda ‘yan Boko Haram suka yi sansanoni. Wani da ya gane wa idanunsa, yace an kashe daruruwan ‘yan bindigar har ma da wasu matansu. Da ma mazauna garuruwan dake kewaye da wannan daji sune suka fi fuskantar hare-haren ‘yan Boko Haram.

Wasu mutane a arewacin Najeriya su na ci gaba da maganar cewa da walakin game da tarobn kasa da ake shirin farawa, cikinsu har da Farfesa Ango Abdullahi na kungiyar dattijan arewa. Idan Allah Ya kai mu ranar litinin mai zuwa za a fara gudanar da wannan taron.

Matsalar karancin man fetur a Najeriya tana kara bazuwa da kara yin muni, inda a Abuja, babban birnin tarayya, aka rika sayar da shi a kanNaira 140 kan kowace lita, wasu ma har fiye da 200 a kasuwannin bayan fage.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Sojoji Sun Shiga Dajin Sambisa; Taron kasa Ko Taron Jonathan; Karancin Mai A Abuja - 1'30"