LAFIYARMU: Kayyade Iyali Na Taimakawa Mata Wajen samun Ingancin Rayuwa

Your browser doesn’t support HTML5

An dade ana muhawara kan kayyade iyali. Wadanda su ke bayan matakin suna masu ra’ayin cewa, yana taimakawa wajen samun ingancin rayuwar mata da yara da kuma bunkasa tattalin arziki. Wadanda kuma su ke gaba da tsarin kuma galibi suna yi ne bisa dalilai na addini ko al’ada.