LAFIYARMU: Yara Masu Matsalar Nakasar Kwakwalwa A Kamaru Na Neman A Kai Musu Dauki

Your browser doesn’t support HTML5

A kasar Kamaru, yara masu fama da larurar nakasar kwakwalwa na fuskantar tsangwama yayin da suke mu'amulla da sauran jama'a. Wannan larura kan sa masu fama da ita su rika kasa sarrafa wasu sassan jikinsu ko su rika yin makyarkyata, a wasu lokuta ma har da farfadiya. Masu gangamin neman a kai wa irin rukunin yara dauki sun ce har yanzu akwai sauran aiki a gaba a kokarin da ake yi na shawo kan kalubalen da masu wannan larura kef ama da ita.