Likita a Liberiya ta Yanke Shawarar Killace Kanta Saboda Ebola

Babbar jami'ar Likita a Liberiya ta yanke shawarar killace kanta na tsawon makwanni uku, bayan da cutar Ebola ta hallaka daya daga cikin masu mata hidima.

Bernice Dahn ta gaya wa manema labarai jiya Asabar cewa babu alamomin cutar a jikinta, to amma ta na so ta tabbatar cewa ba ta dauke da cutar tukun. Ta kuma umurci sauran ma'aikatanta su zauna a gidajensu na tsawon kwanaki 21, wanda shi ne tsawon lokacin da cutar ke daukawa kafin ta bayyana a jikin mutum.

Ranar Jumma'a Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce mutane wajen 150 ne cutar ta kashe a Liberiya cikin kwanaki biyu kawai. Ta ce mutane sama da 1,800 sun mutu sanadiyyar wannan cutar tun bayan bullarta.