Babban Limamin birnin Minneapolis a Amurka yayi tir da Allah waddai da yadda mayakan kungiyar Daular Islama ke fille kanun mutanen da suke kamawa su na yin garkuwa da su, ya ce ba yin hakan ba ya cikin abubuwan da addinin Islama ya umarta da aikatawa.
Sheikh Abdirahman Omar ya fadawa Sashen Somali na Muryar Amurka cewa bisa tsarin dokar Islama, wadanda aka kama a yaki, su na da 'yanci kuma bai kamata a kashe su saboda kasar da suka fito ba.
Ya kamanta Daular Islama da kungiyar al-Shabab ta kasar Somaliya, wadanda ya ce suna yiwa addinin Islama illa da bakanta shi fiye da baiwa mutane sha'awar shiga addinin.
Yace sun kashe duka masu koyar da ilimi, sun kashe manyan masana, sun kashe Limamai a cikin Masallatai. Sun kashe mutane masu dimbin yawa, dimbin mutanen da ba su taka ba, ba su zubar ba. A lokaci guda kuma su rika cewa wai su ceton mutane su ke yi. Sun kashe Musulmi fiye da kowa. Su na muzanta addinin Islama, su na bakanta addinin Islama."
Sheikh Omar ya ce akwai bukatar jami'an gwamnatin Amurka suka kara kokarin nuna cewa ba da addinin Islama Amurka ke yaki ba.
Sheikh Omar ya kara jaddada irin karan tsanar da ake dorawa Musulmi a Amurka, musamman ma tun bayan hare-haren ta'addancin ranar 11 ga watan 9 na shekarar 2001, ya ce abubuwa irin su rukunin wadanda aka haramtawa tafiya ta jiragen sama, da yin tambayoyin ban tsoro game rayuwar Musulmi, da zurawa Masallatai ido da satar sauraron maganganun Musulmi.
Ya ce bullar duka wadannan abubuwa sun sa ana jin kamar da Musulmi Amurka take yaki. Ya ce wannan ra'ayi shi ya sa ake samun karuwar masu zuwa su na taya masu tsattsauran ra'ayi yaki a fagen daga.