Lionel Messi ya Sake Yin Amai, a Tsakiyar Fili - 06/03/14

Lionel messi yana haraswa a wasan sada zumuncin da Argentina ta yi da Romania a Bucharest Larabar nan.

Wannan ba shi ne karon farko da gwanin dan wasan tamaula na kasar Argentina yake haraswa a tsakiyar fili ana wasa ba, 'yan Super Eagles kuyi hattara lokacin gasar cin kofin duniya!

Argentina ta yi kunne doki jiya laraba da kasar Romaniya a wasan sada zumuncin da suka yi a birnin Bucharest, sai dai Lionel Messi bai iya jefa kwallo a raga ba, domin 'yan Romaniya sun hana shi sakat.

Wasan ma dai bai fara tafiya daidai ma gwanin dan kwallon kungiyar Barcelona ta Spain ba domin a cikin minti na 7 da fara wasan sai aka gan shi a fili yana rike ciki, yan asunkuyawa yana amai.

Duk da haka dai, Messi yayi ta maza ya ci gaba da wasa, har ma aka yi aka gama da shi a ciki.

Amma kuma wannan ba shi ne karon farko da Lionel messi yake haraswa ba, idan aka duba tarihi:

1. A shekarar 2011, yayi amai a lokacin da suke bugawa da kungiyar Real Madrid na cin kofin Zakarun kulob-kulob na kasar Spain
2. A watan Maris na 2013, yayi amai a lokacin da Argentina take karawa da Bolivia
3. A watan Agusta na 2013, yayi amai a lokacin da Barcelona ta ke bugawa da Levante

Daya daga cikin kungiyoyin da Lionel Messi zai fuskanta a gasar cin kofin duniya a kasar Brazil a bana, ita ce Super Eagles ta Najeriya!

Hattara dai!.