Liverpool ta ba Manchester United Kashi - 16/03/2014
WASHINGTON, DC —
A wasan da masana tamaula suka ce zai iya zamowa karon battar firimiya lig a bana, 'yan wasan Liverpool sun nunawa Manchester United cewa su ba kanwar lasa ba ce.
Liverpool ta doke Manchester United da ci uku da babu (3-0), ta kuma tsallake Manchester City a zaman ta biyu a saman teburin lig na Ingila da wannan nasara da ta samu.
Gerrard ya jefa ma Liverpool kwallaye biyu a mintuna na 34 da kuma 46 da fara wasa, dukkansu a bugun fenariti. Kamar yadda ya farfado daga rashin jefa kwallaye a wasansu da Southampton kuma, Suarez ya jefa kwallo na uku a ragar 'yan Manchester United a minti na 84 da wasa.
Arsenal ta doke Tottenham Hotspurs a wasa na karshe yau lahadi.
Your browser doesn’t support HTML5
Manchester United Ta Sha Kashi A hannun Liverpool - Lahadi 16/3/2014 - 1'00