Mai Zai Faru da Tattalin Arzikin Najeriya Idan Buhari Ya Zama Shugaban Kasa?

Janar Muhammadu Buhari a Gombe Fabrairu 3, 2015.

A wani zaman tattaunawa da janal Muhammadu Buhari yayi da wasu matasan Najeriya, a wani gidan talabishin dake jihar Lagos, sun dai tattauna kan fannoni da dama, daya daga cikin abubuwan da sukayi magana akai shine kan tattalin arzikin Najeriya.

Kasancewar tattalin arzikin Najeriya na cikin halin ‘daka mai muya, idan aka duba yadda danyan man fetur ya fadi da kashi hamsin cikin dari, kuma arzikin man fetur din nan shine hanyar da Najeriya ke samun kundin ta da kashi saba’in cikin dari. Matasan na son su sani me zai faru da tattalin arzikin Najeriya idan har janal Buhari ya zama shugaban kasa?

Buhari yace abinda zamuyi cikin gaggawa shine duba harkar noma da hakar ma’adanai, dalili kuwa shine tunda muna da kasa kuma muna da mutane, sauran abubuwa kuwa kamar Ilimi da fanin kiwon lafiya sai an shirya tsari domin zasu dauki lokaci da kuma kudi. Tsayar da cin hanci da rashawa zai taimaka kwarai da gaske, kuma za’a iya amfani da ire iren kudaden nan don bunkasa sauran fannoni. Da akwai abubuwa da dama da zamu iya yi domin inganta tattalin arzikin Najeriya, ba wai kawai sai an dogara da man fetur ba, noma, hakar ma’adanai da tsayar da cin hanci da rashawa.