Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya Ta Bukaci A Shawo Kan Cutar Polio

Ana ba ma dan yaro maganin cutar polio

Majalisar dokoki ta tarayyar Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakain shawo kan kan yaki da cutar shan inna.

Majalisar ta bayyana takaicin ganin duk da yawan magungunan rigakafi da gwamnatin tarayya take ba gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi, har yanzu an kasa shawo kan cutar polio.

Shugaban majalisar dattijai David Mark a cikin wani jawabi ya bayyana cewa, abin kunya ne cewa Najeriya tana daya daga cikin kasashe uku na duniya da har yanzu ake fama da cutar shan inna. Ya kuma zargi gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi sabili da kasa marawa kokarin gwamnatin tarayya baya a yunkurin shawo kan cutar.

Bisa ga cewarshi, bai kamata su rika jiran gwamnatin tarayya ta tanada maganin allurar rigakafi ko tsaida lokacin rigakafin ba.

An sami kananan yara tara dauke da kwayar cutar shan inna a jihohi hudu na Najeriya da kuma birnin tarayya Abuja bana.