Malaman Sabuwar Jami’ar Jihar Kano Sun Fara Yajin Aiki

Tattaunawar Shugaba Buhari da VOA Hausa Kan Ziyararsa A Amurka

Yau Kungiyar Malaman Sabuwar Jami’ar koyon aikin malanta ta Kano zata fara yajin aikin gargadi na mako guda,domin nuna bacin ransu game da matakin gwamnatin tarayya na soke Jami’ar tare da takwarrorinta dake Zaria da Owerri da kuma Ondo, da mayar dasu matsayinsu na baya wato kwalejojin ilimi.

Dangane da haka masana a fagen ilimi suka fara sharhi akan alfanu ko akasin sa dangane da wannan matakin na gwamnatin najeriya.

A hirarsu da wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari, Farfesa Salisu Shehu na Jami’ar Bayero Kano, kwararre kan nazarin aikin malanta ya bayyana cewa, daga matsayin wadannan kwalejojin ilimi alfano ne a fannin harkokin ilimi kasancewa kasar tana bukatar karuwar jami’oi, idan za a kwatanta da adadin jami’oin dake kasashen da basu kai Najeriya yawan al’umma da kuma karfin tattalin arziki ba. Ya bayyana takaicin ganin yadda ‘yan Najeriya ke zuwa karatu kasashen da basu kai Najeriya ba,

Farfesa Shehu ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar kwararrun malamai. Yace babu jiha a arewacin Najeriya da zata buga kirji tace tana da kwararrun malamai a dukan kwasakwasai da maddodi na karatu da ake yi, wannan yana nuna, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta tsaya tayi karatun ta-natsu, ta nazarci wadannan matsaloli kafin a yanke hukumci.

Farfesa Salisu Shehu yace idan akwai kurakurai a matakan da gwamnatin da ta gabata ta dauka a wannan fannin ana iya gyarawa a maimakon maida hannun agogo baya.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko daga Kano, Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira Da Farfesa Salihu Shehu-2:53