Manyan Labarai Daga Najeriya a Takaice - 08/03/14

Asabar 8/3/2014
Matsalar karancin man fetur na ci gaba da yin tsanani a Najeriya, kamar a Kaduna inda 'yan Achaba suka ce ba su kara kudin jigilar fasinja ba, amma kuma man ya kai naira 700 kan galan daya. Wani jami'in dillalan mai ya musanta cewa boye man suke yi, duk da cewa ana iya ganinsa ta ko ina a wuraren 'yan bumburutu.

Dan majalisar wakilan tarayya Mahmud Maina daga Borno yace zai gabatar da kudurin dokar ba jama’a ikon rike bindigogi don kare kawunansu, tunda dai hukuma ta kasa kare su.
Mahmud Maina yana wakiltar mazabar Mafa, Konduga da Dikwa a majalisar wakilan tarayya.

A jihar Gombe, an yi wa mata fiye da 100 tiyatar maganin yoyon fitsari. Uwargidan gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo, Hajiya Adama, ta ce su na hada kai da gidauniyar wata jarumar fina-finai domin gudanar da irin wannan aikin.

Your browser doesn’t support HTML5

Manyan Labarai daga Najeriya A Takaice - 1'31"