An kaddamar da Elder, John Maigari, a matsayin mataimakin ‘yar takarar kujerar Gwamna a inuwar jam’iyyar APC, Sanata Aisha Jummai Alhassan, a jihar Taraba.
Kungiyoyin mata a jihar sun nuna farin cikin su da aka samu mace ‘yar takarar Gwamna dake shirin fafatawa da maza a faggen siyasa, kuma matan sun sha alwashin ganin cewa ta samu darewa kan kujerar Gwamnan jihar Taraba.
Dr, Abdulmumini Baki, tsohon shugaban jam’iyyar PDP, a jihar yace a bana kuwa guguwar sauyi ne ke kadawa, ya kuma umarci ‘yan jamiyyar ta APC, sun tabbatar da ganin cewa an hana magudi ta hanyar kasawa da tsarewa.
A nata jawabi ‘yar takarar Gwamna, na jam’iyyar APC, sanata Aisha Jummai Alhassan, ta maida martini ne dangane da korafe-korafe da jama’a keyi cewa bata da miji, tace “ Ni matar aure ce don naji wasu mutanen Taraba suna cewa wai bani da miji, ina da miji, miji na Inginiya Sani Alhassan, mutumin jihar Neja ne yayi ritaya daga aikin Gwamnati yana zaune a Suleja, babu namijin da zai yadda ace yana biye da matar, sa bita zoi-zoi, saboda haka mijina ba mijin Hajiya bane da zai dinga bina koina zani.”
Your browser doesn’t support HTML5
Siyasar Taraba - 3'03"