Akan shirinmu na matasa masu dogaro da kai ko kuma ince tabbatar da cigaban kasa ta fannin illimi, Dandalin VOA ya zanta da wani wanda ke kwararre wajen kirkirar manhaja wato computer software ga ma’aikata wajen tallata kayikansu.
Bello Sani yace da wannan sana’ar tasa dai ya kammala boko, shide Bello Sani yace sana’arsa itace rubuta manhaja ta computer dakuma ta waya da kuma kirkirar shafin yanar gizo, kuma yakai har shekara goma sha biyu yana yin wannan sana’a, Mallam Bello dai baije Jami’a ba yadai je guraren da ake koyarda kosa kosai na na’ura mai kwakwalwa wato computer inda a haka yakoyi wannan sana’ar.
kuma dama can shi mutum ne mai sha’awar yin irin wannan sana’a, wanda ya cimma burinsa alokacin dayake karatu ya kuma fara sana’arsa, ya hada gwiwa da abokinsa inda suka bude kamfaninsu mai zaman kansa, a kamfanin suna kirkirar manhaja ga masu yin sana’a kokuma sauran kamfanoni.
Your browser doesn’t support HTML5
Matasa - 2'19"