Wasu mata sun bayyana bacin ransu a wani gangamin siyasa da akayi game da zargin da suke yi na cewa, ana maida su Saniyar ware da zarar an kammala zabe. Bayan wadannan matsalolin, mata ‘yan siyasa a yanzu na fuskanta suka ga abokannan hamayya ke yi ma ‘yar takara.
Akan haka ne wasu manazarta suke ganin ba aibu in har mace zata tsaya takara muddin dai zata kai jama’arta tudun na tsaira. Lokuta da yawa ‘yan siyasa na daukar alkawalin da ba a cikawa, batun da wasu ‘yan takara irinsu su mai girma Ibrahim Imam me neman zarcewa a majalisar dokokin jihar ke cewa ba haka abin yake ba.
Saurari rahotan Ibrahim Abdul Aziz
Your browser doesn’t support HTML5
Matsalolin Da Mata Ke Fuskanta A Siyasar Najeriya - 3' 02"