Mayar Da Hankali Ga Halin Da 'Yan Gudun Hijira A Fadin Duniya Ke Ciki
Your browser doesn’t support HTML5
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 89.3 ne aka tilastawa barin gidajensu a fadin duniya. Daga cikinsu akwai kusan 'yan gudun hijira miliyan 27.1, kuma kusan kashi 41 cikin 100 daga cikinsu, ba su kai shekaru 18 ba.