A yayin da ake ta shirye shiryen zaben gwamnoni a Najeriya, kungiyoyi da shugabannin matasa da dama a fadin kasar sun yi kokarin kiraye kiraye da gargadi ga matasa musamman domin tabbatar da yin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.
Matasa da dama sun tofa albarkacin bakin su a wata hira da wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir tayi da wasu daga cikin shugabannin matasan. Comrade Abdulmajid Babangida Sa’ad na daya daga cikin jami’an kungiyar matasa mai suna (Kano civil society forum) kuma yayi bayani kamar haka;
“Kullum babbar fadakarwar da muke kokarin baiwa matasa itace muhimmanchin zaman lafiya a kowace al’uma kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe. Kuma lallai muna ganin amfanin abin domin matasa sun nuna amincewar su ga wannan kiraye kiraye ganin yadda babban zaben da ya gabata ya kasance, kuma muna fatan hakan zai dore.
Samun sakamakon abinda jama’a suka zaba dai dai da zabinsu na daya daga cikn makasudin inganta zaman lafiya da fahimtar juna.
Daga karshe shugabannin matasan sunyi kiraye kiraye musamman wajan karbar kudin ‘yansiyasa da wasu matasa keyi domin aikata abubuwan da basu dace ba, wannan yayin ya wuce domin jiki magayi a cewar Sagir Abdu Waziri daraktan kungiyar (youth for human right international).