Mun Kusa Kammala Asibitin Da Babu Kamarsa A Yammacin Afirka – Gwamna Tambuwal

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan jihar Sokoto a Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal ya ce jihar za ta kasance babbar cibiyar samar da likitoci da sha’anin kiwon lafiya a Najeriya da Yammacin Afirka idan sabon asibitin koyarwa mai gado 1500 da kwalejin koyar da aikin likita ta mata zalla da gwamnati ke ginawa suka fara aiki.